Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Jihar Oyo Sun Cafke Mai Safarar Mata


Wasu 'yan Sandan Najeriya a Bakin Aiki
Wasu 'yan Sandan Najeriya a Bakin Aiki

‘Yan Sandan Najeriya sun kama wani Fasto da laifin kai wasu mata ‘yan Najeriya kasar Kuwait da Saudi Arabia da sunan bautarwa a matakai daban daban.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo Alhaji Mohammed Musa Katsina ya fadawa wakilin Muryar Amurka cewa, binciken su ya nuna cewa shi wannan Faston mai suna Adelejah tsohon ma’aikacin banki ne da aka kora bayan samunsa da laifin zambar kudi.

Daga baya ne ya sami waje ya bude coci ya ci gaba da zama. Haka kuma ya bude wani kamfanin tafiye tafiye. Bayan ‘yan sandan sun gano haka ne suka bi sawun wadannan mata har kasar Kuwait da Saudiyya suka kuma zakulo su suka dawo dasu gida Najeriya.

Su kansu matan sun fadi cewa ya yaudare su da cewa zasu yi ayyukan office ne amma sai aka buge da kai su ayyukan barance. Jami’in dan sanda ya bayyana cewa sun kama Faston kuma za su gufanar da shi a gaban shari’a.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG