Bayanai sun nuna cewa maharan sun shiga yankin ne daga Najeriya inda suka kai harin tun a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe tara na dare.
Rahotanni sun ce maharan har ila yau sun yi awon gaba da motoci biyu sun kuma kona wata motar sannan sun kaiwa wasu garuruwa hare-hare da ke kusa da yankin Boso.
Akwai kuma rahotannin da ke cewa maharan sun kwashi kayayyaki da dama a shagunan jama’a baya ga kone-kone da suka yi.
Bayanai na cewa dukannin wadanda suka mutu a hare-haren fararen hula ne kuma babu dakarun kasar ko daya.
Mataimakin gwamnan jihar ta Diffa Lamido Moumouni, ya tabbatar da aukuwar hare-haren inda ya ce gwamnati na kokari ta ga ta samar da cikakken tsaro a yankunan.
A farkon makon nan ne gwamnatin kasar ta Nijar ta baiwa mutanen yankin Tafkin Chadi da su fice daga wuraren, a wani shiri da hukumomi ke yi na kaddamar da hare-hare akan ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
Ga karin bayani a hirar wakilinmu da Abdoulaziz Adili: