Tawagar da ta samu jagorancin Dr Bulama Gubio ta shaidawa Muryar Amurka cewa ta kai ziyara a sansanin 'yan gudun hijira dake jihar Adamawa.
Yawancin wadanda sojoji suka kwato daga hannun 'yan Boko Haram da suka kaisu Adamawa 'yan asalin jihar Borno ne. Tawagar ta je ne domin gani da ido halin da mata da yara sama da dari biyu suke ciki. Daga bisani gwamnatin jihar zata san matakin da ya kamata ta dauka a kansu.
Shugaban tawagar Dr Bulama Gubio yace batun sake masu matsuguni ko mayar dasu gidajensu a garuruwansu na asali ba abu ne na gaggawa ba domin har yansu akwai mayakan Boko Haram boye cikin kurmin Sambisa. Har yanzu 'yan Boko Haram din suna kai harin sari ka noke a kauyuka da ma birane.
Cigaba da samun barazana daga kungiyar Boko Haram ya sa har yanzu gwamnatin Borno na kula da 'yan gudun hijira fiye da miliyan daya a sansanoni sama da talatin inda take kashe fiye da nera miliyan dari shida wajen ciyardasu da samar masu da kayan alatu da suke bukata na yau da kullum.
Akan matsalar Boko Haram na tsawon shekaru shida da suka gabata da yadda suka addabi al'ummar arewa maso gabas, Dr Bulama Gubio yace su da suke jihar Borno yadda suka fahimci 'yan Boko Haram yawancin 'yan Najeriya basu fahimcesu haka ba. Yace idan 'yan Boko Haram suka kama gari aka fatattakesu, ba tafiya suka yi ba. Zasu bazu a cikin daji su hau itatuwa, su shiga koguna tare da mamaye kauyuka su zauna su yi sabon shiri.
Kamar shekaru uku ko hudu da suka wuce mutane sun ga motoci na shiga dajin Sambisa dauke da siminti da rodi da kayan gine-gine amma ba'a ga fitowar motocin ba. Akwai zaton sun gina gidaje a karkashin kasa kamar yadda suka yi cikin birnin Maiduguri. Wanda suka gina a Maiduguri ya dauki mutane fiye da dari biyar. Idan sun gina wannan a garin Maiduguri a idanun mutane babu abun da ba zasu iya yi ba a dajin Sambisa.
Ga karin bayani na Sanusi Adamu.