Zauren Matasa: Matsalar Rashin Aikin Yi Ga Dinbin Matasa Masu Yawa

Matsalar rashin aikin yi ta addabi matasa masu dimbin yawa da suka gama karatu a kusan dukkannin kasashe dake nahiyar Afirka, ba kuma karancin aikin ba ne ya sa haka, galibi matsala ce mai nasaba da cin hanci da rashawa da kuma fifita ‘ya ‘yan manya da ‘ya ‘yan masu fada a ji akan ‘ya ‘yan takalawa.

A cikin Zauren matasa an tafka muhawara ne kan yadda ‘dan talaka ke fama da rashin daidaiton daukar aiki tsakanin su da ‘ya ‘yan manya masu fada aji, ko kuma ‘ya ‘yan masu fada a gidajen manya. Dakta Shariff da jafar jafar sune suka tattauna kan wannan batu.

Mafi yawancin lokuta akan fadawa matasa cewa su nemi ilimi, amma abinda ke faruwa shine dayawa wasu matasan na kallon lamarin ne ta wani bangare na daban, domin zasu ga yadda wani dan talaka zai nemi ilimi ya gama amma babu aikin yi, duk a dalili bashi da wanda zai shige masa gaba wato jagora.

Wannan nauyi ya rataya ne akan duk gwamnatocin kasashen dake nahiyar Afirka, domin su duba yadda zasu samar da wani tsari da zai baiwa kowa yanci neman aiki bisa bin ka’idojin da suka kamata, rashin samar da irin wannan tsari kan iya kara jefa kasashen Afirka cikin cin hanci da rashawa, tare da samun matsaloli a fannin matasa.

Saurari muhawarar.