Rahotanni da dumi dumin su, sun bayyana cewar hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF zata biya sabon kocin da zata dauka tsabar kudi dalar Amurka dubu hamsin $50,000 a ko wane wata, watau kwatankwacin Naira miliyan goma sha shidda kenan wanda ya nunka yadda ake biyan tsohon kocin Stephen Keshi da Sunday Oliseh.
Hukumar kwallon kafar ta dade da fara tunanin daukar kwararren kocin da zai jagoranci kungiyar, kawo yanzu dai hukumar ta riga ta tuntubi tsohon kwac din kasar Cote divore da kasar Zambia Herve Renard da kuma na Uganda coach Micho a makwannin da suka gabata.
Tsohon kwac din kasar jamhuriyar kamaru Paul Le Guen ne na baya bayan nan da ya rage hukumar NFF ta tuntuba, a cewar wata majiya, kwac din A yanzu haka bashi da aikin yi tun watan Nuwambar shekarar data shige bayan korar sa daga aiki.
Shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya bayyana cewa tsohon kwac Sunday Oliseh ne dan gida na karshe da zai jagoranci kungiyar Super Eagles bayan rikon kwaryar jagorancin kungiyar da hukumar ta ba Siasia.