Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren Matasa: Kan Zamantakewar Aure Da Hanyoyin Gyara Aure


A wata muhawara da wakiliyar Murayar Amurka, Madina Dauda, ta jagoranta tare da wasu mata matasa inda suka tattauna kan zamantakewar aure da neman hanyoyin da gyara zaman ma’aurata.

Shin kome me matan dake cikin wannan Zauren Matasa ke gani game da ire-iren halaiyar wasu mazaje na neman matansu a duk lokacin da suka bukata ba tare da yardar mace ba, kuma wasu mazan ba ruwansu domin ko mace tana so ko bata so dole ne ta saurare su, wanda hakan ake yi masa fassara da cewa ya zama fyade.

A cewar daya daga cikin matan dake wannan zaure tabbas ana iya kiran wannan a matsayin fyade, domin a duk lokacin da namiji zai nemi matarsa ta ki ya kuma saka karfi, tabbas bayan ya gama zai iya ji mata rauni wanda hakan zai jefa matar cikin wani hali na daban ya kuma saka mata tsoro da fargaba, a maimakon soyayya.

Tsoro da fargabar miji na iya haddasa kiyayya a tsakanin ma’aurata, wanda kan iya zama sanadiyyar rabuwar aure.

Darajanta mace dai shine miji ya san yadda zai kula da matarsa, wajen sanin abinda take so da abinda bata so da zamantakewar rayuwa, hakin miji ne tabbatar da kwanciyar hankalin matasar ta hanyar tabbatar da cewa ya fita hakkin ta kamar yadda addini ya tsara.

Domin karin bayani saurari hirar zauren matasa.

XS
SM
MD
LG