Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano ta bukaci masu hannu da shuni da hukumomin da ke da alhakin kula da makarantu a jihar Kano da su hada hannu da karfi domin lalubo matsalolin da ke haddasa gobara a makarantun kwana a jihar.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jahar ta ba daliban makarantar GGC Gezawa tallafin katifun kwana, da bokatai, da kwanonin cin abinci da matashin kai a sakamakon tashin gobarar da yayi sanadiyyar konewar dakunan kwanan daliban.
A yayin da ake ta cece kuce dangane da abubuwan da ke haddasa gobara a dakunan kwanan daliban shugabar makarantar ta musanta zargin da ake cewa ko wutar lantarki ce ta haddasa gobarar inda ta ke cewa kimnain shekaru biyar kenan makarantar bata da wutar lantarki.
Ga cikakkiyar hirar da wakiliyar dandalinvoa Baraka Bashir tayi da wasu daga cikin daliban da suka sami wannan tallafi da kuma shugabar makarantar