Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakatar Da Wasu Jami'an Hukumar Kwallon Afirka Ta Kudu


An dakatar da tsofaffin jami’an hukumar kwallon kafa ta Afirka ta kudu a sakamakon zargin su da magudin canza lokacin da ya kamata a buga wani wasa kafin lokacin wasan da aka buga na gasar cin kofin duniya na shekarar 2010 ba bisa ka’ida ba.

Bincike ya nuna cewa hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta tabbatar da dakatar da jami’an na Afirka ta kudu su uku a sakamakon canza lokacin wani wasa da aka buga kafin wasannin cin kofin duniya na shekarar 2010 wanda ba bisa ka’ida ba.

An dakatar da chief Leslie Sedibe tsohon shugaban hukumar ta (SAFA) da haramta mai sa hannu a duk wata harka da ta shafi wasannin kwallon kafa har na tsawon shekaru biyar da kuma cin shi tarar kudi dalar Amurka dubu ashirin da dari biyu da tamanin da shidda ($ 20,286).

Sai kuma Steve Goddard da Adeel Carelse wadanda suka yi wa hukumar aiki a matsayin shugabanin alkalan wasa na tsawon shekaru biyu.

Rahotannin shekarar 2012 daga hukumar SAFA sun bayyana cewar wasannin da ake zargin sun hada da wasan kawance da kungiyar ‘yan wasan kasar ta buga Tsakani ta da kungiyar ‘yan wasan Guatamala da Combiia.

Wasan ya karkare ne kwallaye biyar da babu da Afirka ta kudu ta jefa a ragar takwararta Guatamala a cikin watan Mayu na shekarar 2010, inda aka sa alamar tambaya akan wasu bugun daga kai sai mai tsaron gida guda uku da alkalin wasan nan Ibrahim Chaibour dan kasar jamhuriyar Nijer ya jagoranta. Da kuma nasarar da Bafana Bafana ta samu na ci biyu da daya akan Colmbia.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG