Kafar sadarwar nan mai farin jini wadda ake aika sakon kar ta kwana WhatsApp yanzu haka ta shiga fagen daga da gwamnatin Amurka kan bude wata manhajar da take kare asirin sakon mutane, batun da yazo daidai dana kamfanin apple.
Gidan jaridar Newyork times ne ya ruwaito cewar wani alkalin gwamnatin tarayya ne ya yanke hukuncin cewar jami'ai zasu iya saka ido kan duk wani sako da aka aika ta hanyar sadarwa idan ana binciken wani babban laifi, amma manhajar whatsap.
Wasu jami'ai dai sun bayyana cewa ya kamata kamfanoni irin wadan nan su rika bada hadin kai a duk lokacin da ake binciken wani laifi, amma babu tabbacin hakan zai iya yiwuwa.
An umurci kamfanin apple ya budewa masu bincike wata wayar iphone dake rufe ta matashin nan da ya hallaka mutane da dama a jahar Sanbanadino ta kasar Amurka.
Yanzu haka whatsap nada yawan mutanen dake amfani da shafin a duk wata kusan Biliyan daya, amma jaridar Times ta ce shi wanad ya kafa WhatsApp baya goyon bayan a saka ido akan wannan kafa. har yanzu dai ba'a san wanne irin bincike ake gudanarwa ba, amma akwai rahotannin dake cewa bashi da alaka da ta'addanci.
A farkon watannan ne a kasar Brazil aka garkame wani ma'aikacin facebook akan irin wannan dambarwa inda aka umurce shi da ya bude shafin wani mutum da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi. kamfani twitter da goole da fecebook dai sun nuna kin goyon bayan bude wadannan manhajoji da jami'an tsaro ke kokarin yi.