Wasu da dama kuma sun jikata biyo bayan tashin bam a wurin da ake tantance ma'aikata a sakatariar karamar hukumar Sabon Garin Zaria dake jihar Kaduna yau Talata.
Sheidun gani da ido sun ce bam din ya tashi ne bayan da wurin ya cika dam da mutane wannan Talatar. Wani yace yana tsaye kafin ya ankara sai ya ji karar fashewar bam wanda ya tayar da wani sama. Yace shi ya dauki 'yan jirajirai da aka tantance iyayensu da suka mutu ko suka jikata.
Sabon kantoman riko na karamar hukumar Injiniya Muhammad Usman yace yana cikin ofishinsa lokacin da bam din ya tashi. Ya ji ana gayawa gwamnan jihar cewa mutane 25 suka mutu kana wasu fiye da 30 suka jikata.
Shugaban majalisar dokokin jihar dan asalin karamar hukumar Alhaji Aminu Abdullahi Shagali yace wani bala'i ne ya faru. Yace majalisarsa zata ba gwamnati duk hadin kan da take bukata kan lamarin.
Shi ma gwamnan jihar Nasiru El-Rufai ya ziyarci wurin domin ya gani ma idonsa. Gwamnan yace abun ban tausayi ne da kuma ban haushi. Ya godewa shugabannin asibitin ABU da al'umma da suka fito suna bada taimako ma wadanda suka jikata.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.