Wasu da gwamnatin jihar Kaduna ta baiwa alhakin tantance da mikawa ma'iakata takardun kudi sun yi korafi akan ma'aikatan saboda matsalar sake suna kamar wanda a takardar gwamnati sunasa Abdullahi Sani amma kuma ya zo da suna Abdullahi Junaidu.
Aikin tantance ma'aikatan da zai dauki lokaci yana fama da ccekuce daga wasu ma'aikatan. Sun ce suna yin sammako tun safe su dinga zaman dirshan amma daga bisani kuma ba za'a kula da su ba saboda cinkoson layi. Wasu sun ce sai layi ya kawo kansu a ce su dawo wanshekare amma kuma idan sun zo ba zasu samu ba.
Wasu ma'aikatan da suka sakaye sunanyensu sun yi karin haske. Wani yace makonsa na biyu ke nan da zuwa tantancewar. A wannan karon yana kan layi har ya zo kusa da karshe saura su hudu a gama dasu sai aka ce masu su dawo washegari. Ko da suka dawo wanshekare bukatarsu bata biya ba. Su wadannan har yanzu basu samu albashinsu na watan da ya gabata ba.
Wasu matsalar sunayensu banbancin "e" ne ko "h". Ire-irensu an tara takardunsu kuma babu tabbacin za'a biyasu. Wasu kuma naura ce bata aiki yayinda aka kawo kansu.
Wadanda aka ba aikin tantance ma'aikatan sun ce basu da hurumin sauraren wani korafi. Wai basu da ikon yin hakan.
Shugabar kungiyar malamai a karamar hukumar Igabi Hajiya Rakiya Ubale Adamu tana cikin masu tantance ma'aikatan kuma tayi karin haske akan wadanda aka tantance. Tace wadanda suke da matsala sun basu hakuri su dakata sai an gama da wadanda basu da matsala kana su bisu daya bayan daya.
Samuel Sama'ila Aruwa ya bayyana manufar gwamnatin jihar. Yace gwamnati tana son ta san zahirin gaskiyar adadin ma'aikatanta a matakin jiha da kananan hukumomi ashirin da hudu..
Ga rahoton Lawal Isa Ikara da karin bayani.