Duk da alwashin da Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya yi na cewa ba za’a yi zanga-zanga a jihar ba, mata da matasa sun cika manyan titunan biranen Kaduna da Zariya domin bin takwarorinsu a sauran sassan Najeriya wajen bayyana damuwar su kan matsalar tsaro da tsadar rayuwa.
Sai dai kuma duk da ya ke an yi zanga-zangar ta ranar farko aka kammala lami lafiya a Zariya, a cikin garin Kaduna zanga-zangar ta juye ya zuwa lalata kayan gwamnati da wasu jami'an tsaro.
Mata da matasa sun fito cikin lumana da hadin kai suka fara zanga-zangar a cikin garin Kaduna har zuwa wani lokaci, kafin daga bisani aka sami wasu matasan da su ka fara jefe-jefe a kofar gidan gwamnatin jihar, wanda hakan ya sa jami'an 'yan-sanda su ka fara harba barkonon tsohuwa.
Bayan tarwatsa masu zanga-zangar daga kofar fadar gwamnatin ne sai su kuma matasan su ka fara afkawa ofisoshin wasu hukumomin gwamnatin jihar Kaduna da ke kusa, kamar dai yadda mai-magana da yawun rundunar 'yan-sandan jihar ta Kaduna ASP Mansur Hassan ya shaidawa Muryar Amurka.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar da aka fara cikin lumana sun nuna damuwa kan yadda ta juye zuwa tashin hankali daga baya.
Sai dai kuma a lardin Zazzau an yi zanga-zangar lami lafiya, inda har sai da mai martaba sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli ya fito, ya karbi koken masu zanga-zangar kuma ya yi musu jawabi.
Kwanaki goma ne masu zanga-zangar kuncin rayuwa suka diba na kasancewa akan tituna, to sai dai kuma ganin yadda zanga-zangar ta juye zuwa barna a wasu yankunan, ya sa wasu sun fara shakkar yiwuwar kwashe kwanakin goma ana zanga-zangar.
Saurari rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna.
Your browser doesn’t support HTML5