Kamar dai sauran biranen Najeriya da aka samu sukunin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa, a birnin Legas ma tun da sanyin safiya ne masu zanga-zanga suka fara taruwa a anguwar Ikeja domin fara tattaki zuwa wajen taron jama'a na Gani Fawehmi da ke Ojota domin gudanar da jawabai da kuma bayyana korafe-korafensu ga gwamnati.
Shi dai wannan dandali shi ne wata kotun Legas ta ba da umarnin a gudanar da zanga-zangar a jihar.
Dubban masu zanga zanga da suka samu rakiyar 'yan sanda a karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sandan Legas Adegoke Mustapha ya ce komai na tafiya kamar yadda aka tsara ba tare hargitsi ba- yana mai cewa ba mu da matsala da su kana ganin yadda muke masabaha da juna, komai na tafiya a bisa tsari.
Sai dai sabanin yadda aka san birnin Legas wajen hada-hadanr ababen hawa da na jama'a, a yau birnin ya kasance cikin wani yanayi da jama'a suka kauracewa tituna da kasuwanni da wajen aiki, hattta bankuna sun kasance a rufe.
Ko da yake an shirya zanga zangar ne na kwanaki 10 daga 1 zuwa 10 ga watan nan, masu sharhi da kare hakkin bil adama na cewa dole ne yan Najeriya su tauna tsakuwa domin aya taji tsoro kamar yarda kwamred Musa Jika yake cewa, yace kundin tsarin mulki ya baiwa kowane dan kasa yancin zanga zanga dole ne gwamnati ta bada damar gudanarwa. Hakan shine zaisa q kaucewa fito na fito tsakanin masu zanga zangar na lumana.
Zanga zangar Endsars da ta gudana a Legas da wasu biranen Najeriya a shekarun baya ta haifar da rikici da hasarar rayukan da har yanzu gwamnati ke musantawa.
Yanzu dai fatan yan Najeriya shi ne kammala wannan zanga-zanga cikin kwanciyar hankali ba tare da hasarar rayuka ko samun rauni ba.
Saurari cikakken rahoto daga Babangida Jibrin:
Dandalin Mu Tattauna