Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saka Dokar Takaita Zirga-zirga Ta Sa'o'i 24 A Birnin Kano


Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf (Hoto: Facebook/Abba Kabir)

Gwamnan ya ce majalisar tsaro ta jihar Kano ta amince da wannan mataki kuma dokar ta fara aiki nan take.

Gwamnatin jihar Kano ta ayyana dokar takaita zirga zirgar Jama’a a birnin da kewayen Kano tsawon sa’o’i 24.

Gwamnan jihar Abba Kabiru Yusuf ya sanar da haka ga taron manema labarai a gidan gwamnati.

Ya ce matakin ya zama wajibi la’akari da sabon salon da zanga zangar ta dauka wajen lalata dukiya da kadarorin gwamnati da na al’uma.

Gwamnan ya ce majalisar tsaro ta jihar Kano ta amince da wannan mataki kuma dokar ta fara aiki nan take.

Ya bukaci al'umar jihar su baiwa hukumomin tsaro hadin kai da goyon bayan daya kamata.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG