Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum Takwas Suka Mutu A Zanga-Zangar Jihar Neja - Rahotanni


Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Bayanai daga jihar Nejan Najeriya na nuna cewa kimanin mutane 8 suka mutu a zanga-zangar adawa da matsalar yunwa da tsadar rayuwa da ta barke a ranar Alhamis a sassan kasar

Rahotanni daga yankin Suleja sun nuna cewa jami’an tsaro suka yi ta harbin bindiga ga masu zanga-zangar a cikin garin na Suleja da kuma wadanda ke kan hanyar Kaduna Road dake kan kokarin zuwa Abuja da Kaduna.

Masu Zanga-zanga
Masu Zanga-zanga

Wani shugaban al’umma a yankin na Suleja da ya bukaci a sakaya sunanshi ya ce mutane uku ne jami’an tsaron suka harbe a cikin garin Suleja yayin da kuma a Kaduna Road mutane biyar.

A karamar hukumar Tafa kuma masu zanga-zangar sun auka sakatariya karama tare da lalata kayan dake ciki inda Barista Musa Kallamu daga yankin ya ce hatta na’urorin kwanfuta na sashen na tara kudaden haraji a karamar hukumar duk an tarwatsasu.

Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Tunda farko dai wasu daga cikin masu zanga-zangar sun ce suna cikin tsananin tsadar rayuwa saboda haka babu ja da baya sai gwamnati ta dawo da tallafin mai cikin hanzari.

Gwamnatin jihar Neja dai ta ce ta na godiya ga al’ummar jihar da ba su fito zanga-zangar ba a inda aka samu matsalolin kuma suna ci gaba da baiwa jama’a hakuri ne.

Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Kwamishiniyar Labarai ta jihar Nejan Hon. Binta Mamman ta tabbatar da mutuwar mutane a yankin na Suleja sai dai ta ce ya zuwa lokacin da Muryar Amurka ke magana da ita mutane biyu ne suka tabbatar da mutuwarsu a hukumance.

Kawo lokacin hada wannan rahoto bamu samu wani bayani ba daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ba, domin kuwa ko kokarin samun kakakin ‘yan sandan jihar Wasiu Abiodun ta wayar Salulu ya ci tura.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Mutum Takwas Suka Mutu A Zanga-Zangar Jihar Neja - Rahotanni
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG