Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Mazauna Turai Sun Bukaci A Kai Zuciya Nesa Game Da Zanga-zangar Tsadar Rayuwa


Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya, Kan Titin Abuja-Keffi
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:24 0:00

Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya, Kan Titin Abuja-Keffi

Wasu ‘yan Najeriyar mazauna wasu kasashe da ke bibiyar al’amuran da ke gudana a kasar da dama sun yarda cewa matsin rayuwar da jama’ar kasar ke fama da ita, wani abin tashin hankali ne da aka jima ba a duba wa ba.

Wasu ‘yan Najeriyar da ke bibiyan al’amuran da ke gudana a kasar, da dama sun yarda cewa matsin rayuwar da jama’ar kasar ke fama wani abin tashin hankali ne da aka jima ba a duba wa ba, sai dai kuma akwai bukatar a kai zuciya nesa in ji Nura Ilıyasu Gagarawa wani dalibin da rikicin yakin Sudan ya tilasta masa komawa karatu a kasar Cyprus.

Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

A Faransa inda ake da dumbin ‘yan Najeriya, wasunsu sun nemi a bi sahu a gudanar da zanga-zangar don jan hankalin gwamnatin shugaba Bola Tinubu, amma masarautar sarkin Hausawan ba ta amince da bukatar ba saboda wasu dalilai da bata bayyanawa Muryar Amurka ba.

Shugaban ‘yan kabilar Ibo kuma jigo a kungiyar ‘yan Najeriya Chief Ojiodu Ambrose Uche Alphonsus a Jamus na ganin halin kuncin da kasar ke ciki ba abu bane da za a ci gaba da kau da kai a wannan karon.

Ya ce jama’a na mutuwa an shiga cikin halin matsi kuma dole ne a hada hannu da gwamnati da talakawa a nemo mafita, ba kamar yadda aka saba kau da kai daga matsalolinmu a baya ba.

Wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Duk da halin da aka tsinci kai a kasar, Dr. Abdurrahman Sani Yakubu, shugaban sashen Hausa na Haramin Makka a Saudiya dai, ya nemi a kara yayyafawa zuciya ruwan sanyi ne.

‘Yan Najeriya dai sun tsinci kai cikin matsi da fatara da yunwa da wasu ke dangantawa da janye tallafin mai da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi jim kadan da shan rantsuwar soma mulki a bara.

Saurari cikakken rahoto daga Ramatu Garba Baba:

‘Yan Najeriya Mazauna Turai Sun Bukaci A Kai Zuciya Nesa Game Da Zanga-zangar Tsadar Rayuwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG