Shugaba Mahammoud Issoufou ya yi wannan furucin ne ko kuma buga kitji yayinda yake gabatar da tsare-tsarensa wa magoya bayansa a yankunan Diffa da Tileberi da Yamai na .
To ko da menen shugaban yake tinkaho? Shugaban yace ya dora ne ga abubuwa uku da zasu bashi damar cimma burinsa.Na farko su ne ayyukan da yace ya yiwa 'yan kasa a shekaru biyar da ya yi yana mulki.Yace yana da goyon bayan jam'iyyu kimanin arba'in. Yau 'yan adawa basu da karfin da zasu kai labari sakamakon rabuwan kawunan da ya addabesu har ma wasu kusoshinsu na ficewa suna kafa sabbin jam'iyyu.
Amma Ibrahim Tampole ma magana a madadin mataimakin sarkin yakin neman zaben Seni Umaru na MNSD Nasara ta 'yan adawa yace kalamun na Mahammoud Issoufou magana ce irin ta 'yan siyasa. Yace yara ne suka tarawa wasu ma har da tilasta masu su yi gangami su sauraresu. Babu yadda wani zai ci zabe a zagayen farko.
Yanzu dai 'yan siyasa sun bazu yankunan karkara inda suke neman kuri'u. Akwai 'yan takara 15 dake neman kujerar shugaban kasa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5