Yace a jihar Maradi gwamnan jihar ya kira duk sarakunan jihar gaba daya inda ya gargadesu da su je su yiwa shugaban kasa mai ci yanzu fafutikar neman kuri'u a zaben watan gobe. Yace kowane sarki an bashi riga tare da kudi jaka goma ta sefa domin ya je ya yiwa shugaba kemfen.
Yace dokokin kasar sun haramtawa sarakunan gargajiya yin siyasa. Ya gargadesu da su yi hattara saboda zasu fuskanci hukuncin doka.
To amma a cewar jam'iyyar PNDS Tarayya mai rike da gwamnati tace 'yan adawa sun jahilci dokokin kasar da tanadin da suka yiwa sarakunan gargajiya a yau.Wai doka ta sake. Yanzu doka ta mayar dasu cikin ma'aikatan gwamnati. Ke nan gwamnati na iya sasu aiki.
Dalili na biyu da zasu iya yiwa gwamnati aiki shi ne hatsarin tsaro da kasar ke fuskanta. Sarakuna suna aikinsu ta ba gwamnati labarin duk abubuwan dake faruwa a garuruwansu.
Tuni jagoran 'yan adawa Alhaji Husseini Umaru ya rubutawa kungiyar sarakunan gargajiya wasika cikinta ya gargadesu da su nesanta kansu daga harkokin siyasa tare da yin barazanar kai maganar gaban kotu..
Kungiyar sarakunan gargajiya tace zata mayarda martani akan lamarin nan gaba.
Ga karin bayani.