Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Su Na Karbar Katunan Zabensu A Damagaram


Eid al-Adha Celebration in Zinder, Damagaram, Niger Republic
Eid al-Adha Celebration in Zinder, Damagaram, Niger Republic

Mutane n da suka yi rajistar yin zabe a Damagaram ta Jihar Zinder a jamhuriyar Nijar, su na ci gaba da zuwa karbar katunan zabensu, a bayan da kwamitin da aka dora ma alhakin rarraba katunan ya mika su ga masu unguwannin dake wannan birni.

Kowane mai unguwa, an ba shi alhakin tabbatar da cewa katunan sun shiga hannayen masu su.

Wakiliyar VOA Hausa, Tamar Abari, ta taras da mutane da dama su na duba sunayensu, a cikin jerin wadanda suka yi rajistar, tare da karbar katunan da zasu ba su damar jefa kuri'a a babban zaben dake tafe.

Wakiliyar tamu ta taras da wata malama tana duba sunanta a jikin kundin wadanda aka kawo katunansu, amma har zuwa lokacin da ta bar wurin wannan malamar ba ta ga sunanta ba.

Wani kuwa da yayi sa'a, ya samu nasa cikin sauki, har ma ya karbi na wani dan'uwansa da ya ba shi iznin ya karba masa.

Baruma, ko mai unguwa, Muhammadu na unguwar Ali Yaro, ya shaidawa wakiliyarmu cewa komai na tafiya daidai. Da ta tambaye shi ko doka ta kyale wani ya karba ma wani kamar yadda ta ga wasu suna yi, sai yace muddin suka tabbatar da cewa lallai wanda ya zo karbar da gaske dan'uwan mai katin ne, su na iya ba shi.

Yace dukkan jam'iyyun siyasa sun turo wakilansu wurin raba katunan, kuma su ma wakilan 'yan unguwar ne, saboda haka su na iya hana wani karbar katin idan har ba su amince da shi ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG