Ministan sadarwar kasar Yahuza Sadisu ne ya bayyana hakan a wata ganawa da ya yi Muryar Amurka.
A farkon makon da ya gabata ne ‘yan adawa a kasar suka yi zargin cewa Issoufou na amfani da sarakunan na gargajiya domin samun nasara a zaben da ke tafe.
A ranar 21 ga watan Fabrairu ake sa ran za a yi zaben shugaban kasa a zagayen farko.
A kuma jiya Asabar ne aka kaddamar da yakin neman zabe a duk fadin kasar inda ‘yan takara za su shiga sako-sako domin neman kuri’u.
A can baya ma ‘yan adawan sun zargi shugaba mai ci da fara gudanar da yakin neman zabensa kafin a kaddamar a hukumance.
Domin jin martanin da gwamnatin ta mayar game da zargin yin amfani da sarakunan gargajiya da ‘yan adawa suka yi, saurari jawabin ministan sadarwa Yahuza Sadisu: