Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Ra'ayoyin jama'a akan zaben kasae


Tambarin Jamhuriyar Nijar
Tambarin Jamhuriyar Nijar

Muryar Amurka ta zagaya ta ji ra'ayoyin 'yan jamhuriyar Nijar akan zaben gama gari na kasar da za'a gudanar wannan watan

Malam Labbo mazauni jihar New York a nan Amurka yace yana son mutanen Nijar su yi zabe mai zuwa cikin kwanciyar hankali da lumana kamar yadda wasu kasashe suka yi inda ko dan tsako ba'a kashe ba.

Yace shugaban kasa na yanzu mai kwazo ne. Bai taba ganin shugaban kasar Nijar irinsa ba. Yace shugaban ma'aikaci ne. 'Yan kasa su yi mashi godiya da sake zabarsa.

Ahmadu mazaunin kasar ta Nijar yace yana son a yi zabe na kwarai. A ba duk wanda Allah ya ba. Kada a yi sata. A yi sahihin zabe tsakani da Allah. Wanda duk ya fadi ya san mutanen kasa basa sonshi. Ya hakura. Kada ya bari mutane su soma kashe-kashe.

Shi kuma Muhammad cewa ya yi basa son fitina. Duk wanda ya ci Allah ya sa a bashi domin a gujewa matsala. Yana ganin jam'iyyar CDS Nasara ta Abdu Labbo ya kamata ta ci domin shi Abdu Labbo shugaba ne mai adalci, mai adalci wanda jama'a ke so.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG