Zabtarewar Kasa Ta Kashe Akalla Mutane 93 A Indiya

INDIA - Jihar Kerala Gundumar Wayanad

A yau Talata jami’ai suka bayyana cewa, zaftarewar kasar da aka samu a wurare da dama a kudancin Indiya ta hallaka mutane 93 sannan ana fargabar kasa ta birne wasu mutanen da dama.

Lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan saman da ya sabbaba ruwa da tabo yin awon gaba da rukunin gidajen “Tea Estate” na ma’aikatan gonakin ganyen shayi da wasu kauyuka.

India - Zaftarewar Kasa

Zabtarewar kasar ta afkawa yankuna masu tsaunuka dake gundumar wayanad ta jihar kerala da safiyar yau Talata, inda ta rushe gidaje tare da tumbuke bishiyoyi harma da lalata gadoji.

India - Wayanad Yuli 30, 2024.

Ma’aikatan ceto na kokarin zakulo daga karkashin tabo da baraguzan gine-gine, sai dai aikin nasu na gamuwa da cikas sakamakon toshewar hanyoyi da yanayi na tsaunuka. Har yanzu hukumomi basu kai ga tantance yawan barnar da iftila’in ya haddasa ba.

Minista mai kula da yankin Kerala, Pinarayi Vijayan, ya bayyana cewar zaftarewar kasar ta hallaka akalla mutane 93 sannan fiye da mutane 100 na samun kulawa likitoci akan raunukan da suka ji. Ya kara da cewa an mayar da fiye da mutane dubu 3 zuwa sansanonin bada agaji.

INDIA

Sai dai Vijayan bai fayyace adadin mutanen da suka bata ko baraguzai suka birne ba.

Kafafen yada labaran yankin sun ruwaito cewar galibin mutanen da al’amarin ya rutsa dasu ma’aikatan gonakin ganyen shayi ne dake zaune a rukunin gidajen “Tea Estate”.

INDIA - Jihar Kerala gundumar Wayanad

Hukumomi sun tura jiragen sama masu saukar ungulu domin taimakawa aikin ceto kuma rundunar sojin Indiya ta shigo cikin aikin domin gina gadar wucin gadi.

-AP