Masu harsashen kan yanayi sun bayyana jiya asabar cewa, ana kyautata zaton ci gaba da tafka ruwa na tsawon kwanaki. Masu aikin ceto suna kokarin ceto sama da mutane dubu hamsin da ruwan ya datse a jihar Himalayan dake Uttarakhand, inda ruwan da aka rika tafkawa ya cinye kauyuka baki daya.
Masu aikin ceto rayuka sun ce sun taimakawa sama da mutane dubu talatin su isa wurin da zasu fake cikin kwanaki biyar da suka shige. Wadanda ambaliyar ruwan ya shafa sun hada da masu ayyukan ibada dake kan hanyarsu zuwa wuraren ibadar Hindi da kuma ‘yan yawon bude ido, wadanda sai da aka yi amfani da jirgi mai saukar angulu kafin a ceto su.
Kasar Indiya ta sha fuskantar ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa, sai dai bana ruwan ya sauko mako guda kafin lokacin da aka yi harsashe, abinda ya sa mutane suka rika gudu suna neman mafaka a tuddai yayinda tekuna suka rika ambaliya.