ZABEN2015: Rawar Da Kafofin Sada Zumunta Na Zamani Ke Takawa

Tambarin kafar sada zumunta ta Twitter

Yayin da Najeriya ke tunkarar zabukan 2015 a ranar 28 ga wannan wata na Maris, masana na ci gaba da yin tsokaci kan yadda kafofofin sada zamunta na zamani ke taka rawa.

Kafofin sada zumunta na zamani da suka hada da Facebook da Watssap da Instagram da sauran su na taka muhiummiyar rawa a fagen siyasar Najeriya, in ji masana.

A lokuta da dama jami’yyu na amfani da wadannan kafofi wajen tallata manufofinsu yayin da a wasu lokuta wasu ke ikrarin cewa ana yin amfani da kafofin wajen cin zarafin abokanan hamayya.

Duk da haka, masana da dama na cewa ana amfani da su wajen samun labarai kan abubuawan da suke faruwa.

“Wadannan kafofin sada zumunta suna taimakawa sosai, idan kuma ka duba wani zai shiga irin wadannan kafofi ya yi abin da bai kamata ba.’ In ji Gyang Pam, wani mai sharhi kan al’muran yau da kullum.

Shi kuwa Malam Muhammad Isma’il cewa ya yi “ana samun labarai kan yadda jam’iyu ke yada manufofinsu.”

A cewarsu ko a kasashen da su ka ci gaba kamar Amurka an yi amfani da ire-ire wadannan kafofin yada labarai kuma sun taka muhimmiyar rawa.

Ganin cewa kafofin yada labarai na da matukar muhimmanci ya sa wasu jami’iyyu suka bude nasu gidajen yada labarai musamman kamar yadda jam’iyyun adawa ke ikrarin cewa ba a basu damar yada manufofinsu a kafofi irinsu rediyo da talbijin.

Masana na kallon wannan matakin bude kafafan yada labarai a matsayin wani abu da ya zama dole, domin a cewarsu tura ta kai bango.

Yanzu haka babbar jam’iyar adawa ta APC, ta bude wani gidan rediyo da ke yada manufofinta yayin da ake tunkarar zabuka.

“Abin da ya janyo hakan shi ne babu dama a baka lokacin da z aka fadi dalilan ka na shiga siyasa ka yiwa magoya bayanka jawabi yadda ya kamata.” In ji Alhaji Umar Dan Kano, shugaban wakilan kafofin yada labarai a Jahar Adamawa.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN2015" Rawar da kafofin sada zumun ta zamani ke takawa