Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Masu Ruwa da Tsaki a Harkokin Zabe Sunyi Taro a jihar Niger


Masu ruwa da tsaki a zaben Jihar Niger sunyi taro.

Rundunar yan sandar jihar Niger tayi taro da masu ruwa da tsaki akan babban zabe mai zuwa, a karshen taron dai da aka gudanar a garin Kontagora jamiyyun siyasa sun rattaba hannu akan wata takarda da zaa gudanar da zaben lafiya ba tare da tada hankalin jamaa ba.

Mataimakin kwamishinan yan sanda Mr. Williams Adebowale yace yan sandar nada rawar takawa wajen ganin anyi zaben cikin kwanciyar hankali, yace saboda haka ne aka shirya wannan taron, ga dai abinda yake cewa.

‘’Gaba daya ina bukatar shugabanni harda na addini dasu yi wa matasa nasiha da kar su dauki ko wane irin makami a lokacin da ake gudanar da wannan zabe’’

Suma yan siyasar da suka sa hannu a wannan takardan gargadi, ga abinda suke cewa.

Sunana Dr. Aliyu Sabi Abdullahi Baraden Borgu dan takaran sanata Niger North karkashin jamiyyar APC wannan yana cikin ko wane abinda dan Najeriya ke son ya gani saboda haka abinda ya faru 2011 shima abin darasi ne’’

‘’Sunana Alhaji Usman Magaji Tafidan Nasko Vice Chairman PDP Magama Local Government dalilin da yasa muka sa hannu a kasar nan yau, mu PDP da muke mulki musammam jihar Niger munfi kowa son zaman lafiya’’

Suma shugabannin addinai da suka halarci taron sunyi tsokaci a wajen wannan taron

‘’Nine Aliyu muhammed Sani Adarawa shugaban majilisar malamai ta Jamaatul Izalatul Bidia Waikamatul Sunna Niger-State, gaskiya taron yana da matukar muhimmaci kuma na fahinci akwai tsari mai kyau da su jamiaan INEC suka yi amma kuma akwai jan aiki a gaban su, kuma akwai jan aiki a gaban Police akwai jan aiki a gaban yan siyasa’’

‘’Sunana Nasir Hamza Ina wakiltan masallacin Jumaa dake nan GRA dake cikin garin Kontagora taro yayi kyau ga abubuwan da suka fada, to sai dai dama ba abubuwan da ake fada ba amma abubuwan da ake aiwatar wa kuma kamar yadda ka sani anan kasar tamu ba masu bamu wahala kamar jamiaan tsaro da kuma su yan siyasa da ace abubuwan da suka fada zasu rika tsayawa akan su da an samu saukin al’amurra’’

Mataimakin shugaban kiristoci Senior evangelist da ya halarci taron ga shawarar da ya baiwa yan siyasa.

‘’Shawara ta ga yan siyasa shine kar su yarda su daurewa matasa dake tada fitina gindi da zai wargaza zaman lafiya.’’

A taron babban jamiin hukumar zabe Yusuf Mohammed ya dauki dogon lokaci yana fede biri har wutsiya game da yadda za a gudanar da zaben musammam akan naurar nan mai tantance masu jefa kuria wadda ake cewa Card Reader a turance.

Masu Ruwa Da Tsaki A Zaben Jihar Niger Sunyi Taro
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG