Yace zaben yayi matukar birgeshi domin ya zaga ya ga yadda masu kada kuri'u suka shiga layi suka shafe tsawon lokaci saboda sauke yakin kasa da dimokradiya dake wuyansu.
Jakadan Amurka a Najeriya yayi magana da manema labarai a cibiyar sanarda sakamakon zabe ta INEC a Abuja.
Jakadan yace burin Amurka ne 'yan Najeriya su samu nasara a sakamakon zaben bisa tabbatar da zaben gaskiya da adalci. Yace Amurka ashirye take tayi aiki da duk wanda ya lashe zaben shugaban kasa.
Jakadan ya yaba da naurar tantance masu kada zabe. Yace ko shi kansa a mazabarsa dake jihar Virginia babu naurar zabe dake dauke da bayanansa ko kuma alamar yatsun hannu a rajistan zabe.Yace yana taya hukumar zabe da yin anfani da naurar. Yace yana jin zasu duba naurar da yiwuwan yin anfani da ita a Amurka.
Yanzu dai Farfasa Jega yace zai fara bayyana sakamakon zabe daga yau Litinin zuwa gobe Talata.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5