Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: INEC Ta Fara Hada Sakamakon Zaben Jihar Adamawa


Raba kayan zabe.
Raba kayan zabe.

Cikin tsakiyar daren zaben da aka gudanar ne hukumar zabe ta fara hada sakamakon zaben a jihar Adamawa.

Hukamar zabe ta fara hada hancin sakamakon zaben jihar Adamawa.

Kawo yanzu an samu sakamakon kananan hukumomi tara cikin ashirin da daya. An fara ne da karamar hukumar Madagali. Jami'in bada sakamakon zaben ya nemi hadin kan jama'a da 'yan jarida yayinda suke kokarin bayyana sakamakon zaben.

Amma a yankin Mubi an samu hatsaniya lamarin da ya kai ga yin anfani da jami'an tsaro domin kubutar da baturen zaben da aka tura yankin Dr. Amuga Kefi Na Mala. Wai matasan wurin suka ce ba za'a dauki sakamakon zaben a kai Yola ba, ba tare da bayyanamasu sakamakon ba a wurin da suka kada kuri'unsu.

Wakilan jam'iyyun sun ce babu gudu babu ja da baya zasu tsaya har sai an bayyana sakamakon kafin a wuce dasu Yola

Kamar Adamawa haka ma aka samu hargitsi a jihar Taraba. Akwai zargin an yi anfani da takardun sakamakon zabe biyu a Wukari.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG