Rahotanni daga jihar Bauchin Najeriya na cewa an saka dokar hana fita a wasu sassan jihar yayin da sojoji ke fafatawa da mayakan Boko Haram.
Hukumomin jihar sun ce an saka dokar ne saboda a kare rayuka da dukiyoyin mutane.
Wannan saka doka na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke zargin cewa an saka dokar ne saboda a yi magudin zabe, saboda gwamnati mai ci ta ga 'yan adawa na samun nasaara.
Sai dai gwamnatin kasar ta musanta wannan zargi inda su ka jaddada cewa kare rayuka ake so a yi.
A jiya ne ‘yan kungiyar ta Boko Haram su ka kai hari a jihar Gombe da ke makwabtaka da Bauchin lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama yayin da ake gudanar da zabuka.
Hukumar zaben kasar ta tsawaita wa’adin kammala zaben a wasu sassan kasar zuwa yau lahadi bayan da aka fuskanci wasu matsaloli da suka shafi tsaro da jinkirin zuwan kayayyakin zabe.