Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: An Cigaba da Yin Zabe Jiya a Filato


Shugaban hukumar zabe Attahiru Jega.
Shugaban hukumar zabe Attahiru Jega.

Hukumar zabe ta INEC ta tababbatar da rashin gudanar da zabe a rumfuna ashirin a jihar Filato.

Rumfunan zaben suna cikin kananan hukumomi tara ne a jihar ta Filato.

Hukumar ta bada umurnin a gudanar da zaben jiya Lahadi lamarin da zai kammala zaben shugaban kasa da na majalisun tarayya.

A cewar jami'in hukumar zaben Osarakin mai hulda da jama'a ya bayyana sunan kananan hukumomin da suka hada da Kanam, Bassa, Jos Ta Gabas, Jos Ta Arewa, Wase, Kanke, Langtang Ta Kudu, Mangu da Riyom.

Mr. Osarakin yace matsalar ta biyo bayan tangarda da aka samu ta naurar tantance masu kada kuri'a ne da jinkirin da aka samu na kai kayan zabe kan lokaci.

Jami'in yace a yanzu haka basu sami sakamakon zabe ba saboda rashin kammala zaben ranar Asabar.

Wasu da suka kammala nasu zaben sun bayyana gamsuwarsu da yadda aka gudanar da zaben. Daniel Sule yace sun yi lami lafiya. Babu wani hargitsi.Duk wadanda aka zanta dasu sun bayyana gamsuwarsu.

Garahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG