Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Za'a Yi Zaben Wuraren da Aka Dage 11 ga Watan Gobe


Shugaban hukumar zaben Najeriya Prof. Attahiru Jega
Shugaban hukumar zaben Najeriya Prof. Attahiru Jega

Yayinda yake jawabi da manema labarai shugaban hukumar zabe ta INEC Farfasa Jega ya tabbatar za'a gudanar da zabe a wuraren da aka dage zabe 11 ga watan gobe

Farfasa Attahiru Jega yace akwai mazabun'yan majalisar tarayya goma sha uku da za'a gudanar da zabensu ranar 11 ga watan gobe.

Yace tilas ta sanya hukumar dage zaben a wuraren saboda rashin wadatattun kayan aiki.Bakwai daga cikinsu suna jihar Jigawa. Duka wadanda lamarin ya shafa sun amince a dage zaben zuwa watan gobe. Banda mazabun jihar Jigawa akwai mazabar tarayya ta Wukari a jihar Taraba da kuma mazabar Ethiope a jihar Delta.

Farfasa Jega yace dage zaben bai yi masu dadi ba duk kuwa da kokarin da suka yi na ganin alamura sun tafi kamar yadda suka tsarasu. Amma duk da haka an samu cigaba domin kuwa a shekarar 2011 mun dage zabe a mazabun tarayya 60.

Yanzu ana tattara sakamakon zaben daga mazabu daban daban musamman a jihar Kano a daidai lokacin da mutane da dama suka kwashe daren jiya ba tare da sun samu sun kada kuri'unsu ba. Lamarin da ya sa suka fito tun daga asubahin jiya su kada kuri'unsu sabili da zarafin da hukumar zabe ta bayar cewa su cigaba da zaben.

Mata sun yi fitar dango a wannan zaben domin su jefa kuri'unsu.

Garahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG