Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: An Yi Awongaba da Jami'in Zabe da Sakamakon Zaben Wukari, Jihar Taraba


Mukaddashin gwamnan Taraba
Mukaddashin gwamnan Taraba

Ana zaman dardar a yankin Wukarin jihar Taraba saboda awongaba da aka yi da baturen zabe da takarsun sakamakon zaben.

Ana zargin wani minista da jami'an gwamnatin jihar da aikata ta'asar.

Onarebul Ishaya Daniel Gani dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Wukari ya bayyana halin da ake ciki yanzu. Yace bayan an gama zaben ministan da shugaban karamar hukumar suka dauke takardun sakamakon da baturen zabe suka je gidan gwamnati tare da sojoji kana suka hana kowa shiga. Ana zargin sun sauya sakamakon zaben.

Shi ma dan takarar jam'iyyar SDP ya tabbtar da lamarin da ya faru. Yace duk sakamakon zaben sun canza.

To saidai kwamishanan zabe na jihar Taraba yace shi baisan abun da ya faru ba.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG