Miyetti Allah ce kan gaba da kuma tafi dadewa a tsakanin kungiyoyin makiyaya a Najeriya kuma ta na karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Sultan na Sokoto.
Bayan kammala wa’adin tsohon shugaban kungiyar Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru an shirya zabe inda tsohon sakataren kungiyar Baba Usman Ngelzarma ya zama sabon shugaba.
A wani taro bayan zaben Baba Ngelzarma ya nemi hadin kan dukkan makiyayan da alwashin yin duk mai yiwuwa wajen yi musu jagoranci nagari kasancewar sa ba bako ba ne a jagorancin kungiyar.
Daya daga ‘yan takarar Sa’idu Maikano ya yi watsi da sakamakon zaben, ya na mai cewa an dawo da wadanda a ka zubar a wajen tantancewa cikin zaben.
Maikano ya bukaci a soke zaben da kafa shugabannin rikwan kwarya.
Za a jira a ga yanda iyayen kungiyar za su shawo kan wannan kura don karfafa hadin kai a lokacin da makiyaya da ke daji su ke korafin barayin daji sun hana su sakat kuma jagororin birni ba sa kai mu su dauki.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5