Kungiyoyin Fulani da masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen Najeriya sun yi wata ganawa mabanbanta a Abuja da nufin lalubo bakin zarar matsalar tsaro da ke addabar kasar.
Wannan yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar rashin tsaro na 'yan bindigar daji a kasar ke dada kazanta musamman a yankin Arewa maso yammacin Najeriyar da wasu sassan kasar inda ake salwantar da rayukan dabbobi da hana kiwo ga kuma uwa-uba garkuwa da mutane domin karban kudin fansa.
Kungiyar makiyayan ta Miyetti Allah wacce ta duba hanyoyin magance matsalar makiyya da manoma a taron da ta gudanar na yini guda a Abuja ta bakin shugabanta Alhaji Hussani Yusuf Bosso, ta ce wannan masifa da ake ciki ta shafe kowa da kowa don haka dole ne a tashi tsaye don shawo kanta.
A na ta bangaren kungiyar makiyyan dabbobi ta Miyetti Allah kautal hore da ta hada al’ummar Fulani daga yankin kasashe Afirka16 da kwararru a fanin tsaro, da shugabanin addini hadi hada da jami’an gwamnati ta ce ana yawan zargin al’ummar Fulani da harkan ta’addaci hakan ne ya sa ta gayyato masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen kasar don lalubo mafita mai daurewa kamar yanda shugaban kungiyar Alhaji Bello Bodejo ya ce a yanayin da ake ciki baza su zuba ido wannan masifa ta cigaba da faruwa ba don haka suka yi ma taken taron na su da ''fulani ina mafita"
Shi ko Fittacen Malamin addinin islama Sheik Mahmud Gumi wanda ya sha ido hudu tare da ganawa da yan bindigan dajin ya ce wadannan mutane su na bukatar a yi musu wata ma’aikata da za’a ta mai da hankali kan harkokinsu na kiyon da noma a kasar
Ko da yake dai gwamnatin Najeriya ta ce akwai tsare tsare a kasa da aka warewa bangaren noma da kiwo kasar cewar Dr Mohammad Mahmood Abubakar da ke zama ministan noma da raya yankunan karkara a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton da Shamsiyya Hamza Ibrahim ta hada: