Shugaban kungiyar ta Miyetti Allah a karamar hukumar Bassa, Alhaji Ya’u Idris wanda ya bayyana cewa an sami zaman lafiya a yankin, da suke zaton zai dore, ya bayyana takaicinsa kan yadda a cikin kwanakinnan ake sanya wa dabbobinsu guba, suna mutuwa.
A bangare guda kuwa, mai magana da yawun kungiyar raya kabilar Irigwe, Mr Davidson Malison ya ce basu da masaniyar an sanya wa dabbobin makiyayan guba.
Ya kara da cewa yayin da aka kafa kwamitoci don sasanta yadda makiyayan za su shigo kasar Irigwe, wassu makiyayan sun shigo sun barnata amfanin gona wa manoman yankin.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su bada bayani kan lamarin ba, duk da sakon da murya Amurka ta aike wa STF.
Hukumomin gwamnatin jahar Filato da hukumar tabbatar da tsaro ta Special Task Force sun nada kwamitoci daban-daban don kawo karshen tashe-tashen hankula da ake samu tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankin na karamar hukumar Bassa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: