Ta'azzarar matsalar rashin tsaro a Najeriya musamman a yankin arewa da kuma gazawar hukuma wajen dakile matsalolin bai rasa nasaba ga bullar ‘yan sa kai domin su taimaka wajen kare yankunan su daga ayukkan ‘yan fashin daji.
Fulanin sun koka ne biyo bayan harin da 'yan sa kai suka kai makon da ya gabata da ya yi sanadin rasa rayuka da dama.
Duk da sadaukarwar da 'yan yakin sa kai su ke yi wajen yaki da ‘yan ta'adda hakama ana zargin su da wuce gona da iri abinda ya soma tunzura Fulani wadanda ke ganin sune suka fi fadawa tarkon su, kamar abinda ya faru a Sakkwato, makon da ya gabata inda fulani kusan 20 suka hadu da ajalinsu ta hannun ‘yan sakai.
kungiyar-miyetti-allah-a-najeriya-ta-gudanar-da-taron-neman-mafita-ga-fulani
yan-bindiga-sun-kashe-fulani-makiyaya-bakwai-a-filato
yan-bindiga-sun-kashe-dan-majalisar-dokokin-jihar-zamfara-jim-kadan-bayan-bikin-komawa-apc
A hirarshi da Muryar Amurka, Aliyu Busawa sakataren kungiyar miyetti Allah ta Najeriya reshen jihar Sakkwato yace ba za su zura ido suna kallon ana kashe kabilar fulani ba.
A can baya ma wasu gwamnatoci sun haramta kungiyoyin sa kai a jihohin su, saboda gudun kara dwagulewar rashin tsaron .
Kwamishinan tsaro a jihar Sakkwato kanal Garba Moyi Isa Mai ritaya, yace gudun hakan ne ya sa gwamnati ta dakatar da ayukkan ‘yan sa kai sai ta basu zabi.
Wannan rigimar na batun kunno kai lokacin da jama'a basu gama jimamin harin da ‘yan fashin daji suka kai a kasuwar mailalle ba lokacin da take ci da yayi sanadiyar salwantar rayuka sama da 20, abinda gwamnatin tace dama ta hana cin kasuwa don gudun faruwar irin haka.
Masu lura da al'amurra dai na ganin cewa akwai bukatar gwamnati ta kara azama wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro domin kaucewa wasu matsaloli da kan iya kunno kai sanadiyar matsalar ta rashin tsaro.
Saurari rahoton cikin sauti: