IBB ya yabawa 'yan Najeriya da bada hadin kai wurin ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.
Yace sai a godewa Allah saboda mutanen kasar da suka dage zasu yi zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da wata hutsuma ba. Yace a godewa Allah wanda ya ga Janar Muhammad Buhari ya kamata ya zama shugaban kasar a wannan lokacin. Bugu da kari ya godewa shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan wannda yace ya nuna mazantaka sosai. Abun da shugaban yayi ba'a taba yin irinsa ba a duk fadin Afirka. Yace shugaba Jonathan shi ne na farko da ya karbi kadara cewa haka Allah ya yi kana ya kira abokin hamayyarsa ya gaisheshi, ya tayashi murna tun kafin ma a bayyana cikakken sakamakon zaben.
Dangane da inda yake ganin Janar Buhari sai fara mulkinsa IBB yace ya fada. Yace kuma Allah ya taimakemu ya taba yin aikin saboda haka ba sabon abu ba ne a wurinsa. Ya san abubuwan da zai yi.
Gameda dangartakansa da Janar Buhari IBB yace shi ya sha fada ma 'yan jarida. Yace 'yan jarida suke ganin babu jituwa tsakaninsu, amma ba haka lamarin yake ba. Yace aboki ne kuma sun yi yaki da aiki tare. Dukansu sun san martabar kasar da kuma mahimmancin kasar garesu. Yace su da magoya bayansu zasu yi duk abun da zai taimakawa kasar ne.
A wata sabuwa kuma gwamnan jihar Neja Muazu Babangida da ya rasa kujerar majalisar dattawan Najeriya ya rungumi kadara ya kuma yiwa wanda ya samu nasara fatan alheri.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5