Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

zaben 2015: Legas Ta Yi Maraba da Janar Buhari


Masu goyon bayan Buhari a Legas
Masu goyon bayan Buhari a Legas

Tun bayan da aka ayyana Janar Muhammad Buhari a matsayin shugaban kasa mai jiran gado ne magoya bayan jam'iyyar APC suka fantsama kan tituna suna farin cikin nasarar jagoran nasu.

Zaben dai ya cika da sarkakiya idan aka yi la'akari da yadda aka jinkirta zaben da wasu kalamun tada hankali da zaman dardar da 'yan Najeriya suka shiga ciki.

To amma matakin da shugaban kasa mai barin gado Goodluck Ebele Jonathan ya dauka na mika fatar alheri tare da amincewa da sakamakon zaben ya gama tarihi a siyasar ta Najeriya.

Al'ummar yamma maso kudancin Najeriya inda mataimakin shugaban kasa na Janar Buhari ya fito su ma ba'a barsu a baya ba wajen bayyana farin cikinsu da wannan nasara.

Tun jiya ne aka fara wasannin ababen hawa a biranen Legas da kewaye domin nuna farin cikinsu da wannan nasara.

Alhaji Muhammad Bello wani shugaban al'umma ne a birnin Legas wanda ya yaba da yadda aka gudanar da zaben. Yace abun da ba'a yi tsammani zai faru ba ya faru domin ba'a san shugaba mai ci yanzu zai yi muba'aya dangane da sakamakon zaben ba tare da ja ba.

Wani mazaunin layin Ikorodu ya bayyana nashi ra'ayin. Yace abun da ya bashi mamaki shi ne shi bai taba ganin irin wannan bikin ba a Najeriya.

Alhaji Inuwa Yahaya na jam'yyar APC cewa ya yi nasarar daga Allah take.

Ga rahoton Babangida Jibrin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG