Da yake bayyana cikakken sakamakon zaben shugaban kasa ha harshen turanci da aka gudanar ranar Asabar da ta wuce da kuma Lahadi a wasu wuraren, Farfasa Attahiru Jega shugaban hukumar zabe ya bada adadin kuri'un da kowane dan takara ya samu daga jami'iyyu 14.
Ganin babu wani dan takara da ya samu kuri'un a zo a gani baicin 'yan takaran APC da PDP hankulan jama'a sun koma ne kansu kawai.
Farfasa Attahiru Jega yace a matsayinsa na babban jami'in zaben shugaban kasa ya tabbatar cewa dan takarar jam'iyyar APC Janar Muhammad Buhari ya samu kuri'u miliyan goma sha biyar da dubu dari hudu da ashirin da hudu da dari tara da ashirin da daya wato 15,424,921.
Shi kuma dan takarar jam'iyyar PDP Goodluck Jonathan ya samu kuri'u miliyan goma sha biyu da dubu dari takwas da hamsin da uku da dari daya da sittin da biyu, wato 12,853,162.
Wato dan takarar APC ya doke na PDP da kuri'u miliyan biyu da dubu dari biyar da saba'in da daya da dari bakwai da hamsin da tara wato 2,571,759.
Farfasa Jega yace a matasyinsa na jami'in zabe Janar Muhammad Buhari ya cika duk ka'idodin zaben saboda haka ya bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben. Daga yau Janar Buhari ya zama shugaban kasa mai jiran gado.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.