ZABEN2015: Meyasa Hafsoshin Tsaro Basu Amsa Gayyatar Majalisa Ba?

Ginin majalisun tarayyar Najeriya.

Bayanai daga Majalisar Dokokin Najeriya sun ce hafsoshin suna shirin ganawa da shugaba Jonathan tukuna, kafin su amsa goron gayyatar majalisar.

Tun bayan da majalisun dokokin kasa suka koma bakin aiki a makon jiya, ake ta magana kan lokacinda manyan hafsoshin rundunonin tsaro zasu bayyana gaban majalisa, domin suyi karin bayani kan dalilan dage zabe, al'amari da aka aza kansu, cewa ai sune suka rubutawa shugaban hukumar zabe takarada suna masu cewa ba zasu bada tabbacin samar da tsaro ba.

Da yake magana kan wannan batu Senata Mohammed Umar Bago, yace hafsoshin sun ce wata sabuwa ta taso wacce zata bukaci su gana da shugaban kasa Goolduck Jonathan, kamin su bayyana gaban majalisa tukuna.

Senata Bago yace suna kuman jin jita-jitar cewa akwai wani shiri daga bangaren zartaswa na neman zuwa majalisa saboda a nemi hadin kansu na neman sabon, ko karin wa'adi, na watakil a sake dage zabe. Ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, wannan bukata idan har an gabatar musu da ita, to da ita da wacce za'a kira matattar-abu daya ne.

A nasa gefen, senata Kabiru Gaya, yace da farko dai an yi kuskure na dage zabe ba tareda an tuntube su ba.

Senata Gaya yace babu hurumin amfani da soja a harkar zabe, domin wannan aikin 'Yansanda ne.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Hafsoshin tsaro basu amsa gayyatar 'yan majalisun kasa ba.