Shugaban jam'iyyar na jihar Adamawa Chief Joel Hamanjore Madaki ya bayyana matakin da zasu dauka.
Yace kowa dan isaka ne. Horaswar iyaye da addini suka canza mutane. Da ya juya kan shugabannin kananan hukumomi sai yace rahoton da suka samu sun nuna cewa suna yiwa jam'iyyar zagon kasa. Haka ma kansiloli. Suna jam'iyyar ne da bakinsu amma zuciyarsu na wata jam'iyyar.
Shi ma gwamnan jihar Bala James Ngilari ya bayyana abun da zasu yi. Kana ya mayarda martani wa wadanda suke cewa bai tabuka komi ba. Yace duk wadanda ba zasu yi Jonathan da Nuhu Ribadu ba su fice daga jam'iyyar tun da sauran lokaci.
Wai da kudi ake cin zabe. Wadanda zasu bada kudin suna nan. Idan an kawo yace zai basu rabonsu su je a yi yakin zabe a kuma ci. Akan 'yan ta'adan Boko Haram yace ko ba'a yaba mashi ba sun koresu saura tashi karamar hukumar.
Shi ma Malama Nuhu Ribadu dan takarar gwamnan jihar a karkashin inuwar PDP cewa yayi suna da shugaban kasa mai son Adamawa. Wai shugaban kasa ya kama bakinsa da ya fada masa cewa babu abun da gwamnatin tarayya tayi a jihar.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.