Daidaikun jama’a da wasu kungiyoyi masu zaman kansu na amfani da dage zaben Nijeriya da aka yi wajen fadakar da mutane muhimmancin zaben. Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin wasu bayanai ke nuna cewa har yanzu wasu da dama a karkara ba su je su karbi katunan zabensu ba.
Wani jigo a Cibiyar Tabbatar da Shugabanci na Gari Da Cigaban Yankunan Karkara ta “Rural Integration and Development Initiative” Alhaji Muhammadu Danduram na ganin lallai fa akwai abin dubawa kuma da bukatar a kara azama wajen wayar ma mutanen karkara kai. Wannan, in ji shi, shi ya sa ma su ka tashi haikan wajen fadakar da al’umma.
Wakilinmu na jihar Adamawa wanda ya aiko ma na da wannan rahoton, Ibrahim Abdul’aziz, ya ruwaito wasu nakasassu, ciki har da Liviticus Jajije da Matudi Ali, na nuna damuwarsu kan yadda su ke ganin na’urar da aka samar ba ta iya daukar bayanan hannayensu sosai saboda kanta da kuma dungu. Don haka, su ka ce ya kamata a saukaka masu ta wajen tsara wata hanya ta dabam wadda nakasarsu ba za ta hana ta daukar bayanansu ba. Shi kuwa wani manomi mai suna Danjuma Babati kira ya yi ga talakwa ‘yan’uwansa da su kasance masu hakuri sosai don ganin an yi zaben da su.