Mutane da dama suna fargaba, suna ganin za'a iya kawo wani dalili na sake dage zaben karo na biyu.
Amma 'yan siyasa basa ganin wani dalilin sake dage zaben. Sai dai fatan alheri suke yi. Duk da hakan wasu da aka zanta dasu sun je ba za'a yi zaben ba.
AQbdullahi Ali Kano na kwamitin kemfen din shugaba Jonathan yace rashin zaben na kawo masu tsaiko wajen ayyukan raya kasa. Yace a nasu bangaren basa shakkar zabe. Jinkirin ma da aka samu ya dada dakatar dasu ne saboda abubuwan da suka tsara zasu yiwa 'yan Najeriya da tuni sun dade suna yinsu. Abubuwan sun shafi layin doko, noma, taki da dai sauransu. Zabe ma tankar sun riga sun ci ne.
Ibrahim Abdulkarim babban jami'i na tarawa Janaral Buhari gudummawa yace 'yan Najeriya sun gaji da gwamnatin Jonathan. Abun da ya sa 'yan Najeriya basu shiga rigima ba akwai ranar 29 ga watan Mayu da alatilas shugaban kasa na yanzu zai kau. Tun lokacin da ya hau mulki bala'i ya aukawa kasar.
Amma wasu 'yan PDP na ganin tsayar da shugaba Jonathan shi ya kawowa jam'iyyar cikas. Jibrin Zakar Jigawa yace sun riga sun makara babu wata shawara da zasu bayar saidai jam'iyyar ta hakura a yi zabe kuma duk wanda yaci a bashi kana jam'iyyar ta je ta sabunta halinta.
Ga rahoton Nasiru Adamu EL-Hikaya.