Wasu jiragen sama biyu masu launin soji, sun yi ta watsar da takardu masu dauke da sakonnin kungiyar Boko Haram a kananan hukumomin jihar Adamawa, inda a ciki ta ke nemar gafarar jama’a saboda gallaza masu da ta yi.
Wakilinmu na jihar Adamawa wanda ya aiko da rahoton Ibrahim Abdul’aziz ya ce an rubuta sakonnin ne cikin harsunan Turanci da Hausa da kuma Larabaci. Wasu da su ka samu sakonnin sun ce an gaya ma jami’an tsaro kuma sun ce kar a damu.
To amma Ibrahim ya ruwaito Muhammad Abdulhamid na Cbiyar Cigaban Al’umma na ganin shirya abin aka yi don a dauka cewa sojoijin Nijeriya na kokari sosai. Ya ce amma hakan daga baya kan zama yaudara. Ya kawo misali da kashe Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau da sojojin Nijeriya su k ace sun yi, wanda daga baya aka ga bah aka ba ne; ya kuma ce a wasu lokutan ma sojojin Nijeriya sun yi ikirarin kwace wasu wurare amma daga baya ya zama karya.