Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Gwamnan Jihar Neja Yayi Jifar Matattan Mage


Gwamnan jihar Neja
Gwamnan jihar Neja

Dr Muazu Babangida Aliyu na jihar Niger ya mika ragamar mulkin jihar ga kakakin majilisar, a dai-dai wannan lokaci da takaddamar siyasa take kara zafi tsakaninshi da mataimakinshi, Ahmed Musa Ibeto.

A cikin satin data gabata ne gwamnan jihar Niger Dr Muazu Babangida Aliyu na jihar Niger ya mika ragamar mulkin jihar ga kakakin majilisar jihar ga shugaban majilisar dokokin jihar Barister Adamu Usman, inda wasu kafofin yada labarai na Najeriya suka ruwaito gwamna Babangida Aliyu yana cewa mataimakin nasa baya kasar, abinda yasa ya mika ragamar mulkin jihar ga kakakin majilisar.

Wannan al’amarin yasa mataimakin Gwamnan Alhaji Ahmed Musa Ibeto kiran taron manema labarai, inda yace tabbas ya rubutawa gwamnan Babangida Aliyu takardan neman iznin yin tafiya zuwa kasar waje har sau biyu amma bai bashi iznin yin tafiyar ba kamar yadda yake cewa.

“Hasali ma ranar da yayi tafiyar nan ina nan kasar”

Da kuma aka tambaye shi to ko yanzu menene matsayin sa? Anan sai mataimakin gwamna Alhaji Ahmed Musa Ibeto yace, ‘’Matsayina dai shine kamar yadda aka gani ban dai yi tafiyar ba, ina cikin kasa kuma gashi ya mika mulki ga kakakin majilisa kuma zamu zauna a jamiyya musan wani mataki ne zamu dauka’’

Tuni dai al’ummar jihar suka fara furta albarkacin bakin su akan wannan dambaruwa, shugaban kwamitin yada labarai na majilisar dokokin jihar Niger Honarabul Bello Agwara ga abinda yake cewa “Shi gwamna fa shi ke da wannan alhakin da ya kamata ya duba shin mataimakin sa ne yakamata ya rike idan zaiyi tafiya ko kuwa kakakin majilisa’’

Barister Abdulmalik Sarkin Daji lauya ne anan jihar Niger kuma ya duba wannan batu a kundin tsarin mulkin Najeriya ga kuma Karin hasken da yayi “Doka ta ba matainakin gwamna dama ya aiwatar da duk abinda gwamna zai aiwatar idan gwamna basi nan, shi doka taba dama shi kundin mulki Najeriya ya ba dama, shi kakakin majilisa doka bata bashi wannan damar ba, idan ga mataimakin gwamna a raye, kuma yana a jiha, yana a kasa’’

Barister yace ba zabi bane na gwamna kundin mulki na Najeriya yayi bayani dalla dalla akan hakkin gwamna da mataimakin sa, da kuma shi kakakin majilsa na jiha.

Mataimakin Gwamnan dai Alhaji Amhed Musa Ibeto ya canza sheka ne zuwa jamiyyar adawa ta APC, abinda yasa jita-jitan cire Ibeton ta fara yaduwa a jihar.

To sai shugaban majilisar dokokin dake rike da mukamin mukaddashin gwamnan a yanzu Barister Adamu Usman yace babu wannan shirin.

GWAMNAN JIHAR NEJA - 3'39"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG