Hukumar Zabe ko INEC ta fara bayyana sakamakon zaben 'yan majalisar tarayya a jihar Neja.
Ana kuma tattara sakamakon wasu 'yan majalisar daga wasu kananan hukumomin jihar.
Sakamakon kujerar sanata daga yankin gabashin jihar Neja na nuna cewa an samu sakamako daga kananan hukumomi guda takwas daga cikin kananan hukumomi tara. Sakamakon ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar APC David Umaru na kan gaba da gagarumin rinjaye da kuri'u 197435 yayinda gwamna Muazu Babangida Aliyu ke da kuri'u 65742. Amma ana jiran sakamakon karamar hukumar Rafi.
A wani gefen kuma baturen zaben Farfasa Nsofo ya sanarda kujerar majalisar wakilai na yankin Boso da Paikoro inda ya bayyana cewa Onarebul Salihu Adamu Shabafo na APC ya samu kuri'u 59256 sannan Onarebul Abdullahi Kwatu na PDP ya samu 16938. Saboda haka ya bayyana Salihu Shabafo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Hukumar zaben na cigaba da karbar sakamakon zaben shugaban kasa daga kananan hukumomin jihar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5