ZABEN2015: Boko Haram ko Gwamnati Ce ta Kai Hari Gwambe?

Sojojin Najeriya suke sintiri.

Manjo Yahya Shunku mai ritaya yace akwai bukatar 'yan Najeriya suyi nazarin harin da aka kai Gwambe.

Wani mai fashin baki kan harkokin tsaro, Manjo Yahya Shunku mai ritaya, yace batun tsaro da ake yi arewa maso gabashin Najeriya ya shafi jihohi uku ne; Barno, da Yobe da kuma Adamawa. Jihohi da ake maganarsu kan dalilan dage zabe.

Amma a cikin wasikar da hafsoshin tsaron Najeriya suka rubutawa shugaban Hukumar Zabe kan dalilan dage zaben, sun saka Jihar Gwambe a ciki. Ya kara da cewa, yayinda ake tambayar su dalilan sanya Gwambe a ciki jerin jihohi masu fama da matsalolin tsaro, kwatsam sai gashi an kai hari a jihar.

Manjo Shunku yace ganin yadda suka sanya Gwambe a ciki, tilas suna da masaniya game da harin da aka kai jihar. Idan haka ne, su da suke ikirarin zasu magance rikicin Boko Haram cikin makonni shida, me yasa duk da alamun sun san cewa za'a kai harin, basu dauki mataki na hana kai harin ba, kuma da aka kai harin duk da jami'an tsaro da aka girke sun kasa kama koda mutum daya duk lokaci da 'yan binidgar suka dauka suna yada farfagandarsu kan zabe?

Manjo Shunku yace saboda ma a gane cewa wannan ba harin Boko Haram bane, abunda Boko Haram bata taba yi ba, sai gashi wai tana raba kasidu tana barazanar afkawa wadanda suka fito domin zabe.

Yace ko gwamnati taso ko bata so, wannan harin dai na Gwambe akwai alamun tana da hanu ciki.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram ko Gwamnati Ce ta Kai Hari Gwambe? - 5'37"