Kungiyoyin kiristocin sun goyi bayan Mr. Darius Isyaku dan takarar jam'iyyar PDP mai neman ya zama gwamnan Taraba a zabe mai zuwa.
Wasu suna ganin matsayin da kungiyoyin suka dauka bai dace ba ganin cewa jihar Taraba ta kunshi musulmai da kiristoci da dama.
To amma shi dan takarar na PDP Darius Isyaku, ya ce akwai rawar da kungiyoyin addini za su taka a harakar zabe. Domin haka babu laifi su fito su nuna inda suka sa gaba ko suka tsaya.
Yanzu haka 'yan siyasa da wasu kungiyoyi sun soma mayar da martani akan wannan batun.
Kungiyar kawo fahimtar juna tsakanin musulmai da kiristoci a jihar tana ganin bai dace ba wata kungiyar addini ta fito ta ce tana goyon bayan wata jam'iyyar siyasa.
Godwin Jonah na kungiyar ya ce abubuwa da dama na faruwa a cikin jihar da basa faranta masu rai ko kadan.
Matsayin da kungiyar kiristoci ta dauka bai kawo gyaruwar kasar ba-inji Jonah, Ya kuma karyata ikirarin da kungiyoyin kiristoci suka yi.
Jonah ya kara da kiran 'yan Taraba da su hada kai su roki Allah ya basu gwamnatin da za ta yiwa jiharsu aiki, da kuma gwamnatin da za ta rike talakawa ba gwamnatin da za ta saye mutane da kudi ba.
Akan zargi jam'iyyu da yin amfani da addini to amma shugaban APC a jiha, Alhaji Alhasan Jika Ardo ya musanta zargin. Yace yanzu a fili take an san wadanda suke yin anfani da addini suna siyasa. Yace duk wadanda suka san ba zasu ci zabe ba zasu yi anfani da addini da kabilanci.
Ita kuma 'yar takarar kujerar gwamna a karkashin inuwar APC Sanata Aisha Jummai Alhasan ta shawarci al'ummar jihar su kai zuciya nesa. Tace duk shugaban da ya nemi a zabeshi bisa ga addini to baya da niyyar yin adalci kamar yadda addinan musulunci da kiristanci suka koyas. Ta kira mutanen jihar su gujewa addinin siyasa domin tana raba kawunan mutane da haddasa rashin zaman lafiya.
Su ma 'yan sandan jihar ta bakin kakakinta Joseph Kwaji tace ba zata kyale duk wani yunkurin yin anfani da addini ko kabilanci ba.Yace su daina yakin zabe wanda zai kawo tashin hankali. Duk wanda suka kama yana yin abun da zai tada hankalin jama'a zasu hukuntashi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5