A Jihar Rivers da ke Kudu maso kudancin Najeriya, akalla mutane takwas ne suka mutu yayin da ake gudanar da zaben gwamna a jihar.
Rundunar ‘yan sanda Jihar wadda ta tabbatar da aukuwar hakan ta ce baya ga asarar rayuka wasu da dama sun jikkata yayin da aka rasa dukiyoyi da dama.
“An kona motoci kirar bas wadanda suka kawo masu aikin zabe guda uku an kona wata makarantar firaimari da aka yi zabe sannan an kashe mutane bakwai da wani da aka yanke mai kai.” In ji Kakakin runduanr ‘yan sandar jihar River Hassan Karma.
A cewar kakakin, wasu kayayyakin zabe sun kone da dama a wurin da aka dana wani abin fashewa da ya kona motocin.
Har ila yau wakilin Muryar Amurka ya ruwaito cewa an hurga wani abu mai kama da nakiya a kusa da wata tashar zabe a karamar hukumar Amoaha da ke cikin jihar ta Rivers
A jihar Akwa Ibom kuwa da ke kusa da Rivers din, jam’iyyar APC ta yi kira da a soke zaben jihar da na ‘yan majalisun dokokin saboda tashe tashen hankula da aka samu na ‘yan bindiga a lokacin zaben inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi.
Sai dai a daya bangaren jam’iyyar PDP ta ce ita ta lashe zaben jihar saboda haka ba ta kalubalantar sakamakon zaben.
Ga karin bayani daga wakilinmu Abubakar Lamido a yankin Niger Delta:
Your browser doesn’t support HTML5