Malam Tukuntawa yace shugaban kasa mai jiran gado Janar Buhari ya fada a zabi 'yan APC ne saboda jam'iyyarsa ce.
To amma idan ta karan kansa ne Janar Buhari zai ce a tsaya a duba soboda baya. Akwai wadanda za'a zabesu taren amma sabili da halinsu ba daya ba ne zasu koma inda suka gani ya fi dace masu. A ra'ayin Tukuntawa a bi cancanta ba jam'iyya ba.
Amma shugaban matasan arewa na maja ya goyi bayan kiran da Janar Buhari yayi dari bisa dari. Ra'ayin 'yayan jama'iyyar APC ya rabu akan zabe bisa ga cancanta ko jam'iyya.
Wasu suna ganin jam'iyyar PDP ta mutu gaba daya yayinda wasu kuma suna cewa ba za'a ce jam'iyyar da tayi mulkin kasa har tsawon shekaru 16 ta mutu ke nan. Abun da ya faru an canza gwamnati daga hannun Jonathan wanda ya gaza ya kuma sake gazawa. Amma ba za'a ce ta mutu ba.
A harakar zabe ba'a hana mutum ya zabi abun da yake so ba. Saboda haka za'a samu wuraren da PDP zata dan ci ko yaya aka yi.
Alhaji Habu Karami Jahun jigo a jam'iyyar PDP reshen jihar Jigawa yace an zabi Janar Buhari shugaban kasa Allah ya sa fatan da ake yi masa ya tabbata. Amma kada ya yiwa kasar rufin "kura da gwado". Karami Jahun yace maganar gyara ce ta sa aka kawo Janar Buhari. Jonathan ya kasa gyara Najeriya. Ya bari ta tabarbare duk da kiran da manyan jam'iyyar suka yi na ya kawo gyara amma yayi kunnen shegu.
To saidai Jahun yace a jihar Jigawa hankalin jama'a ya kwanta. Duk abun da yakamata a yi an yi. Saboda haka sun san inda zasu jefa kuri'arsu ranar Asabar.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.