Wata dambarwar siyasa da taso tsakanin jam'iyar APC da ta lashe babban zaben Najeriya da aka gudanar kwanan nan itace barazanar da 'yan majalisa 19 a karkashin jam'iyar APC suka yi na tsige gwamna Fayose.
Jam'iyar PDP ta nemi janar Muhammadu Buhari ya shiga tsakani, wakilin sashin Hausa Nasir Adamu El-Hikaya a wani rahotan sa, sakataren labarun PDP Olousameto ya ce gwamna Al'makura ya nemi taimakon sa da kuma na wasu sauran shugabannin PDP inda suka taimaka mashi ba'a tsige shi ba kuma a cewar sa Jam'iyar PDP ta can can ci tukwici a wanan lokacin.
A jahar Zamfara kuma, rahotanni na nuna cewar tsohon gwamnan jahar Muhammadu Shinkafi na jam'iyar PDP wanda ya taba faduwa zabe sakamakon wani sabani da suka samu tsakanin sa da mai gidan sa yariman bahura ke son dawowa a zaben ranar Asabar domin karawa da Takwaransa na jam'iyar APC Abdul'aziz Yari.
Haka irin wannan yanayin yake a Jahar Gombe da ma sauran jahohin da kungiyar Boko Haram ta nakasa, Gwamna Danjuma Goje cwa yayi lallai yayi danasanin dora Gwamna Dan Kwambo dan haka yake goyon bayan jam'iyar APC domin a cewar sa yana kokarin gyara kuskuren da yayi na kawo Gwamnan saboda wasu dalilai da dama na cin amana.
Rahotanni sun nuna cewar hukumar zaben zata yi anfani da na'urar tantance katin zabe a zaben mai karatow kamar yadda akayiamfani da ita a babban zaben kasa da ya gabata.